Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wata motar safa da ke dauke da bakin haure da ke dawowa daga kasar Iran ta kife kuma ta kama da wuta a Herat bayan ta yi karo da manyan motoci biyu da babur. Adadin wadanda suka mutu ya kai 85, yara 17 na daga cikin wadanda suka mutu. Hotunan da aka fitar sun nuna tsananin munin hadarin.
Iran ta jajantawa al'ummar kasar Afganistan sakamakon mummunan hatsarin mota da ya afku a lardin Herat na kasar Afganistan, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu 'yan kasar a yammacin jiya.
A wani sako da ya aike ta shafin Twitter, mataimakin ministan harkokin wajen kasar kuma Darakta Janar na yankin kudancin Asiya, Mohammad Reza Bahrami, ya jajantawa mamatan, ya kuma yi addu'ar Allah ya jikansu, ya kuma yi fatan samun koshin lafiya ga wadanda suka jikkata.
Your Comment